Kewaye da Ni

Kewaye da Ni yana sanar da wurare har guda huɗu da ke kusa da ku: ɗaya a gaba, ɗaya a dama, ɗaya a baya da ɗaya a hagu. Kuna jin kowanne daga ɓangarensa, tare da nisansa. Ku yi amfani da shi don gane inda kuke idan kun isa wani wuri.

Idan kuna tsaye a wuri ɗaya, ku fara nuna saman wayar zuwa inda kuke fuskanta. Idan wayarku a kulle take, ko Soundscape ba ya kan allo, ku kuma riƙe wayar a kwance.


This site uses Just the Docs, a documentation theme for Jekyll.