Shawarwari
Don nemo tashoshin bas na kusa, ku zaɓi Wurare na Kusa sannan ku zaɓi Sufurin Jama’a.
Idan kuna yawan hawa bas ɗaya, ku ajiye tashoshinku a matsayin alamomi. Ku saita sigina a kan tashar da kuke sauka, sai Soundscape ya gaya muku nisanta yayin da kuke cikin bas.
Kuna iya kashe sautin siginar kuma har yanzu ku ji nisan wurin. Soundscape yana faɗin nisan lokaci-lokaci yayin da kuke motsawa.
Don bincika wani wuri kafin ku je, ku buɗe Cikakkun Bayanan Wuri nasa sannan ku zaɓi Kwaikwayi Wuri. Sai Soundscape ya yi aiki kamar kuna can.
Don samun umarnin hanya mataki-mataki, ku buɗe Cikakkun Bayanan Wuri na wani wuri sannan ku zaɓi Buɗe a manhajar taswira. Soundscape yana ci gaba da aiki yayin da ɗayar manhajar take ba da umarni.